11 Disamba 2025 - 14:56
Source: ABNA24
Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Ghana Da Isra'ila Ya Ƙaru Ya Kai Ga Korar ‘Yan Kasashen Biyu

Bayan kamawa da korar 'yan ƙasar Ghana a Tel Aviv, gwamnatin Accra ta kori 'yan ƙasar Isra'ila uku a matsayin ramuwar gayya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta sanar da cewa an kori 'yan ƙasar Isra'ila uku daga ƙasar, kwanaki kaɗan bayan an kama wasu 'yan ƙasar Ghana tare da korarsu a filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel Aviv. Accra ta bayyana matakin a matsayin rashin mutuntaka da rashin adalci.

Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana cewa an tsare 'yan ƙasar bakwai - ciki har da 'yan majalisar dokoki huɗu - na tsawon sa'o'i a babban birnin Isra'ila tun ranar Lahadi da ta gabata ba tare da wani dalili ba kuma an sake su bayan shiga tsakani na diflomasiyya.

An kuma tilasta wa wasu uku korar su a jirgin farko da zai tafi zuwa Accra, matakin da gwamnatin Ghana ta kira mai tayar da hankali ba abun da za a yarda da shi ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ƙara da cewa tawagar 'yan majalisar dokokin ƙasar ta yi tafiya zuwa Tel Aviv don halartar wani taro na ƙasa da ƙasa kan tsaron yanar gizo, kuma mutanen uku da aka kora nan da nan suka koma Ghana.

Ma'aikatar ta jaddada cewa hakan ya tilasta wa gwamnatin Ghana ta mayar da martani iri ɗaya. Za a ci gaba da kare mutuncin 'yan ƙasar Ghana, kamar yadda ake girmama mutuncin 'yan wasu ƙasashe.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ghana ta sanar da cewa an kira babban jami'in diflomasiyyar Isra'ila a Accra saboda rashin jakadan kuma ta gabatar mas da jan kunne mai ƙarfi. Ta kuma jaddada cewa ikirarin Isra'ila na cewa ofishin jakadancin Ghana da ke Tel Aviv ba ya ba da haɗin kai ba shi da tushe kuma ofishin diflomasiyyar Ghana ya kasance yana bin dokokin ƙasa da ƙasa koyaushe.

Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Ghana Da Isra'ila Ya Ƙaru Ya Kai Ga Korar ‘Yan Kasashen Biyu

Dangantaka Tsakanin Ƙasashen Biyu

Ghana da Isra'ila sun kafa dangantakar diflomasiyya bayan samun 'yancin kai na Ghana a 1957, amma an yanke waɗannan alaƙar bayan yaƙin Oktoba na 1973, saboda haɗin kai da matsayin Larabawa. Duk da haka, an dawo da dangantakar Ghana da Isra'ila a 1994, kuma tun daga lokacin, haɗin gwiwa a fannoni daban-daban da tafiye-tafiye akai-akai tsakanin Accra da Tel Aviv ya ci gaba. Duk da karuwar rikicin da aka samu kwanan nan, ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta jaddada cewa bangarorin biyu sun amince su yi kokarin warware rikicin cikin lumana, amma Accra ta jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma nan gaba dole ne ta tabbatar da cewa an girmama 'yan kasar Ghana cikin mutunci, kamar yadda sauran kasashe ke sa ran za a kula da 'yan kasarsu a Ghana.

Your Comment

You are replying to: .
captcha